Kamar yadda mu ke da dokoki a kasarmu domin zaman lafiya da salama, haka nan Allah yana da ka'idodin da dole mu san su idan muna bukatar zaman lafiya da shi.

1.ALLAH YANA KAUNARKA KUMA YANA MIKA MAKA KYAKKYAWAN SHIRI DON
RAYUWARKA.

Game Da Kaunar Allah

"Gama Allah ya kaunaci duniya har ya ba da makadaicin Dansa don dukan wanda ke dogara gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai madawwami." (Yahaya 3:16)

Game da Shirin Allah:

Kristi ya ce, "Dalilin zuwana ke nan in ba da rai a yalwace." (Yahaya 10:10)

Amma mutane da yawa ba sa jin dadm rayuwarsu domin...


2. MUTUM YANA DA ZUNUBI, KUMA YA RABU DA ALLAH, DON HAKA BA YA IYA
SANIN KAUNAR ALLAH DA SHIRIN NAN NA RAYUWARSA.

Mutum Mai Zunubi Ne:

"I, kowa ya yi zunubi, kowa ya kasa ga darajar Allah."
(Romawa 3:23)

Allah ya halici mutum domin yana so ya yi zumunta tare da shi. Amma mutum ya zabi bin nufin kansa, saboda haka zaman lafiya da Allah ya gagare shi. Bin nufin kanmu cikin kowane abu, babba ko karami, shi ne Littafi Mai Tsarki yake kira zunubi. "Dukanmu kamar tumaki muka bata. kowa yana bin nasa tafarki."
(Ishaya 53:6)

Mutum Ya Rabu Da Allah:

"Gama hakin zunubi mutuwa ne (rabuwa da Allah shi ne mutuwa ta ruhaniya."
(Romawa 6:23)

hausa1

Wannan zane yana nuna yadda Allah Mai Tsarki ba ya zama tare da mutum mai zunubi. Kibawun nan suna nuna yadda mutum yana neman zuwa wurin Allah ta kokarin kansa, alal misali. ta hanyoyin addini, da zaman aminci, da addu'a, da taron sujada da dai sauransu. Amma wadannan duka ba za su kai mutum ga ceto ba.

Ka'idan nan ta uku ce kadai ta ke nuna mana hanya daya tak wadda za mu bi don mu koma wurin Allah


3. BA WATA HANYA DA ZA TA KAI MU WURIN ALLAH SAl TA WURIN YESU ALMASIHU. YA MUTU DOMINMU. TA WURINSA KADAI ZA KA IYA SANIN KAUNAR ALLAH DA SHIRIN DA YA Yl DOMIN RAYUWARKA.

Almasihu Ta Mutu Dominmu:

"Allah ya nuna kaunarsa zuwa gare mu yadda Kristi ya mutu dominmu. tun muna cikin zunubi." (Romawa 5:8)

Almasihu Ya Tashi Daga Cikin Matattu:

"Almashiu ya mutu domin zunubanmu ... an binne shi... kuma an ta da shi a rana ta uku. kamar yadda annabawa suka yi annabci." (I Korantiyawa 15:3-4)

Ban Da Yesu Babu Hanyar Ceto:

"Yesu ya ce masa, Ni ne hanya. Ni ne gaskiya. Ni ne rai; ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina" (Yahaya 14:6)

hausa2

Wannan zane yana nuna yadda Allah shi kadai zai jawo mu zuwa ga kansa. Ya aikata wannan sa'ad da ya aiko Yesu domin ya mutu bisa gicciye saboda zunubanmu.

Amma sanin ka'idodin nan uku kurum bai isa ba


4. DOLE KOWANNENMU YA KARBI YESU KRISTI YA ZAMA MAI CETONSA DA UBANGIJINSA; TA HAKA KADAIZA MU SHA DADIN KAUNAR ALLAH DA SHIRIN DA YA Yl DON RAYUWARMU.

Dole Mu Karbi Yesu Ta Wurin Bangaskiya:

"Amma dukan wadanda suka karbe shi, ya ba su iko su zama 'ya'yan Allah ta wurin ba da gaskiya ga sunansa." (Yahaya 1:12)"Sabode alherinsa ne an cece ku ta wurin bangaskiya cikin Kristi ... Ceto ba bisa kokarin kanmu bane, don haka ba mai iya yin fahariya." (Afisawa 2:8,9)

In Za Mu Karbi Yesu Dole Mu Gayyace Shi:

Yesu ya ce. "Gama ina tsaye a bakin kofa (In zuciyarka) ina kwankwasawa; duka wanda ya ji muryata, kuma ya bude kofa zan shiga wurinsa." ( Wahayin Yahaya 3:20)

Karbar Yesu ya shafi gaskatawa cewa Allah zai shiga zukatanmu ya gafarta mana zunubanmu. Dole ne mu juya daga zunubi, mu ba Yesu dama ya yi zamansa a cikinmu.

Wadannan zane-zane suna kwatanta zaman mutum iri biyu:

hausa3

 

1.Zaman Bin Nufin Mutum: Wannan mutum da ikon kansa ya ke bin nasa nufi. Yesu (+) ba ya cikin zamansa. Digodigon nan suna nuna fannonin zaman mutum. Wato kamar addini, da kudi, da ayyuka, da matsaloli, da dai sauransu. Duk wadannan suna karkashin nufin mutum. Duk wadannan suna karkashin nufin mutu. Don haka mutumin nan ba shi da salama. 2. Zaman Bin Nufin Kristi: A nan Yesu (+) ya shiga cikin zaman mutumin nan, yana mulki bisansa. Wannan mutum ya yarda Yesu ya yi mulki bisa kowane fannin zamansa. Don haka ya mika addinisa, da kudinsa, da ayyukansa, da duk an kome nasa karkashin sarautar Yesu. Sabonda haka yana da salama tsakaninsa da Allah.

Daga cikin zane-zanen nan biyu, wannene ke nuna irin zamanka?
Wannene ka fi so ya nuna irin zamanka?

Ga yadda za ka karbi Yesu Kristi:

ZA KA IYA KARBAR YESU TA WURIN BANGASKIYA

In ka gayyace shi ta wurin addu'a ya shigo ranka, ya zama Mai Cetonka da Ubangijinka, kuma ka ba da gaskiya cewa ya shigo, haka kuwa zai zama. Allah ya san zuciyarka, kuma ba ka iya rudinsa ba, domin haka ka ba da gaskiya cikin addu'arka. Ga addu'ar ka za ka yi:

"Ya Ubangiji Yesu, ta wurin bin nufin kaina na yi maka zunubi. Ka shigo zuciyata, ka gafarta mini zunubaina. Ka yi mulki bisa kaina, ka maishe ni sabon mutum. Na gode domin ka amsa addu'ata. Amin.

Kana so ka yi wannan addu'a? In ka yi ta, Yesu zai shiga zuciyarka kamar yadda ya yi alkawari....

Ka kabriYesu yanzu? Yesu na cikin zuciyarka yanzu?Ta yaya ka sani? Ka dubi alkawarin Allah cikin Wahayin Yahaya 3:20. Za ka iya sani Yesu yana cikin zuciyarka domin ya yi alkawari. Ba ka bukatar ka sake gayyatarsa.

KADA KA DOGARA GA YADDA KA KE JI

Yau kana muma, mai yiwuwa ne gobe za ka ji dan bakin ciki. Ko da yaya ka ke ji, Yesu Kristi yana nan cikin zuciyarka, don ya ce, "Ba zan bar ka kai kadai ba." (Ibraniyawa 13:5) Ka dogara ga Maganar (alkawaran) Allah. Kada ka dogara ga yadda ka ke ji.

SA'AD DA KA KARBI YESU KRISTI, ABUBUWA DA YAWA ZA SUFARU ....Ga wadansu:

I. Yesu Kristi ya shiga cikin zuciyarka da zamanka. (Wahayin. Yahaya 3:20)
2. An gafarta maka zunubanka (Kolosiyawa 1:14)
3. An maishe ka daya daga cikin 'ya' yan Allah. (Yahaya 1:12)
4. Kana da rai na har abada. (I Yahaya 5:11-13)
5. Ka fara jin dadin zamanka domin Kristi yana rayuwa cikinka. (Yahaya     10:10; 2 Korantiyawa 5:17)

Wadan nan abubuwa da alkawarai da dama daga wurin Allah naka ne. Ka karanta su daga cikin Littafi Mai Tsarki. Cikin Ayyukan Manzanni 17:11 wadansu mutane suka rika bincike Maganar Allah kowace rana, domin su gane ko gaskiya ce.

SHA WARWARI A KAN YADDA ZA KA Yl GIRMA CIKIN KRISTI:

Ka yi addu'a ga Allah ko wace rana. (Luka 18:1)
Ka karanta maganar Allah ko wace rana. (Zabura 119:11) Ka fara karatu a Bishara ta hannun Yahaya.
Ka yi biyayya ga Allah kullum. (Yahaya 14:21)
Ka shaida Kristi ta wurin zamanka da kuma maganarka. (Luka 8:39)
Ka dogara ga Allah cikin ko wane abu. (1 Bitrus 5:7)
Ka yarda Ruhu Mai Tsarki wanda ke tare da kai yanzu, ya ba ka ikon yin kome a dukan zamanka ko wace rana. (Galatiyawa 1:16,17; Ayyukan Manzanni 1:8)
Muhimmin abu ne ka yi girma cikin Kristi ta wurin kasancewa cikin zumunci da 'yanuwa Kirista (Ibraniyawa 10:25) Ka fara zuwa wurin sujada inda a kan girmama Kristi, ana kuma biyayya ga maganarsa.

Ai ya kamata yanzu ka gaya wa wani labarin nan mai dadi.


 

ADDITIONAL ASSISTANCE